logo

HAUSA

Hukumar kididdigar Sin: Za a daidaita tasirin da COVID-19 ke haifarwa tattalin arzikin kasar

2022-05-16 14:43:42 CMG Hausa

Yayin taron ganawa da manema labarai da aka kira yau Litinin da safe, kakakin hukumar kididdigar kasar Sin kuma shugaban sashen hadaddiyar kididdigar tattalin arzikin al’ummar kasar Fu Linghui, ya yi bayani kan dalilin da ya sa aka yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar zai karu, duk da cewa, ma’aunin tattalin arzikin kasar ya ragu a watan Aflilun da ya gabata, inda ya yi tsokaci cewa, duk da yadda yaduwar annobar cutar COVID-19 a wasu sassan kasar Sin, ta haifar mummunan tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki, tattalin arzikin kasar zai samu ci gaba sannu a hankali, saboda sharrudan ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci ba su sauya ba, don haka tabbas kasar Sin za ta daidaita mummunan tasirin bisa manufofin raya tattalin arziki da na kandakargin annobar da gwamnatin kasar take aiwatarwa. (Jamila)