logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan murnar zama sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa

2022-05-15 20:49:25 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, murnar zama sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa.

Xi ya ce, yana matukar maida hankali kan raya alakokin kasashen biyu, kana, yana fatan kara kokari tare da shugaba Mohamed, don sa kaimi ga ci gaban dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, da samar da alfanu ga kasashen biyu gami da jama’arsu baki daya. (Murtala Zhang)