logo

HAUSA

Kasar Sin Kasa Ce Da Ta Jawo Jarin Waje Da Yawa A Duniya

2022-05-13 21:00:12 CMG HAUSA

Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar a ranar 12 ga wata sun nuna cewa, a rubu’in farko na shekarar bana, jimillar jarin waje da aka yi amfani da shi a zahiri a duk fadin kasar Sin, ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 478.61, wanda ya karu da 20.5% bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Yayin da ake fuskantar yaduwar cutar COVID-19 a gida da wajen kasar da kuma sauye-sauyen da ake fuskanta a kasashen duniya, masu zuba jari na kasashen ketare sun rika zuba jarinsu a kasar Sin, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin kasa ce da masu jarin waje suke nuna matukar sha’awa. Haka kuma lamarin ya musunta rahotonnin da wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suke yadawa, dangane da raguwar kwarewar kasar Sin ta jawo jarin waje.

A rubu’in farko na bana, kasar Sin ta samu saurin karuwar jarin waje a wasu manyan fannoni masu muhimmanci. Yawan jarin da kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da kuma Jamus suka zuba a kasar Sin a zahiri ya karu da 76.3%, 53.2% da 80.4% bi da bi. Sa’an nan kuma yawan sabbin manyan ayyukan da aka zuba jarin waje fiye da dalar Amurka miliyan 100 ya kai 185, kwatankwacin manyan ayyuka 1.5 a ko wace rana. Wannan ya nuna yadda masu jarin waje suke nuna matukar sha’awa kan kasar Sin.

Me ya sa masu jarin waje suke sha’awar kasar Sin? Kamfanin Pricewaterhouse Coopers ya gabatar da wani rahoto a kwanan baya cewa, kasuwannin kasar Sin da bunkasar tattalin arzikin kasar, su ne manyan batutuwa guda 2 da suka fi jawo hankalin kamfanonin kasa da kasa.

Kamar yadda kasar Sin ta yi wa kasashen duniya alkawari, kasar Sin ba za ta rufe kofarta ga kasashen ketare ba, maimakon haka, za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare. Sakamakon aiwatar da yarjejeniyar RCEP, ya sa kasar Sin, za ta kara ba da iznin shiga kasuwannin cinikin hidimomi da zuba jari, za kuma ta kara bude kofa ga waje, lamarin da zai kara bai wa kamfanoni masu jarin waje dama. (Tasallah Yuan)