logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Samun Sakamako Mai Gamsarwa A Wannan Zagaye Na Rigakafin COVID-19

2022-05-13 20:12:59 CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru Jumma'ar nan cewa, bisa kokarin da gwamnati da jama'ar kasar Sin suke yi cikin hadin gwiwa, kasar ta samu sakamako mai gamsarwa a wannan zagaye na rigakafin cutar COVID-19.

Jiya ne shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi karin haske game da Amurkawan da suka mutu sanadiyar cutar COVID-19, wanda ya kai miliyan 1. A halin da ake ciki, har yanzu wasu mutane a Amurka suna sukar matakan yaki da cutar da kasar Sin ke aiwatarwa.

Zhao Lijian ya ce, a ko da yaushe gwamnatin Sin tana dora muhimmanci kan kiyaye lafiyar jama'a, kana tana martaba manufar gano da kuma yaki da annobar baki daya. Haka kuma kasar tana amfani da matakan rigakafi na kimiyya da hakikan matakan kandagarkin annobar don cimma hakikanin nasarar rigakafi da kandagari, ba tare da kashe kudade masu yawa ba.(Ibrahim)