logo

HAUSA

Yanayin Muhallin Kasar Sin Ya Ga Sauyi A Tarihi

2022-05-12 20:34:30 CMG Hausa

Babban jami'i a kwamitin tsakiya kan harkokin kudi da tattalin arziki na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Han Wenxiu, ya bayyana cewa, yanayin muhallin kasar Sin ya samu sauyi a tarihi a cikin shekaru goma da suka gabata.

Han ya bayyana a wani taron manema labarai Alhamis din nan cewa, mun ga karancin kwanaki masu hazo da baki da kuma ruwa mai wari, kuma mun ji dadin sararin sama da ruwa mai haske da kuma tsaunuka masu ban sha’awa.

Ya kara da cewa, gandun daji na kasar Sin da aka kafa, ya kai kusan kashi daya bisa hudu na yawan wadanda ake da su a duniya, kuma hayaki mai gurbata muhallin duniyarmu na CO2 da ake fitarwa ya ragu da kusan kashi 34 bisa dari.

Bugu da kari, kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya, wajen kafa tsarin samar da wutar lantarki bisa karfin iska da sauran makamashi marasa gurbata muhalli, da kuma kera da sayar da motoci masu amfani da sabbin makamashi.

Han ya ce, a matsayinta na mai martaba yarjejeniyar Paris, kasar Sin ta ba da sanarwar kaiwa ga kololuwar fitar da hayaki na CO2 kafin shekarar 2030 da kuma daidaita hayakin da ake fitarwa da wanda ke cikin sararin samaniya nan da shekarar 2060.(Ibrahim)