logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabuwar Shugabar Kasar Hungary

2022-05-10 19:16:29 CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, Talatar nan ya aike da sakon taya murna ga Katalin Novak, bisa kama aiki a matsayin shugabar kasar Hungary.

Xi ya bayyana cewa, ci gaban dangantakar da ke tsakanin Sin da Hungary tana da kyau sosai a cikin 'yan shekarun nan, inda manyan jami’an kasashen biyu ke ci gaba da yin mu'amala mai kyau, da kyakkyawar hadin gwiwa a fannoni daban daban, da yin hadin gwiwa mai kyau a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Shugaba Xi ya ce, yana mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Hungary. Yana mai cewa, a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Novak, wajen zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da sada dadadden zumunci a tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)