logo

HAUSA

Xi ya yi jawabi yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar CCYL

2022-05-10 13:20:44 CMG Hausa

Da safiyar yau Talata ne aka kira babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin ko CCYL a takaice, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar,

Yayin taron, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kana shugaban kwamitin aikin soja na kasar Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi.

Da farko shugaba Xi ya taya murna, tare da bayyana fata alheri ga daukacin ‘yan kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin, da jami’an kungiyar a adadin kwamitin kolin JKS, inda ya yi nuni da cewa, a ko da yaushe matasa suna taka babbar rawa ga ci gaban bil adama, kuma a cikin shekaru 100 da suka gabata, kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta a karkashin jagorancin JKS.

Xi ya jaddada cewa, dole ne a rika yin kokari na cimma burin kasar Sin, kuma ya dace matasan kasar Sin su ba da gudummowarsu wajen farfado da al’ummun Sinawa.

Ya ce, “Ya dace matasa su sauke nauyin tarihi dake bisa wuyansu, matasan kasar Sin suna sanya kokari matuka domin ciyar da kasarsu gaba yadda ya kamata, kamar dai yadda suka bayyana yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

Kana Xi ya gabatarwa kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin fatansa a bangarori hudu. Na farko, kungiyar ta ci gaba da horas da matasa wajen tunanin siyasa. Na biyu ta ci gaba da kasance abun koyi ga sauran matasan kasar. Na uku, ta kara karfafa cudanyar dake tsakanin JKS da matasa. Na hudu kuwa, ta kyautata aikinta a ko da yaushe, ta yadda za ta kasance kungiyar dake tafiya da zamani a karkashin jagorancin JKS. (Jamila)