logo

HAUSA

Sin ta bukaci a tabbatar da hadin gwiwar ci gaban duniya bisa adalci da daidaito

2022-05-10 16:02:49 CMG HAUSA

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi kiran a tabbatar da hadin gwiwar bunkasa ci gaban duniya bisa adalci da daidaito.

Wang ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a babban taro ta kafar bidiyo na kungiyar abokai masu neman tabbatar da ci gaban duniya wato (GDI).

 Ya yi nuni da cewa, sama da kasashen duniya 100 ne suka nuna goyon bayansu, kana jimillar kasashe 53 tuni sun riga sun shiga kungiyar. Wang ya ce, hakan ya nuna cewa, kungiyar GDI tana amsa kira a ko da yaushe, kuma tana biyan muradun kasashe daban-daban.

Game da batun gina tsarin hadin gwiwar bunkasa cigaban duniya bisa daidaito da adalci kuwa, Wang yace, kamata yayi kasashe mafiya karfin cigaba su cika alkawurransu na bayar da tallafin bunkasa cigaba, kana su samar da karin tallafin kudade da na fasahohi.

Wang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashe masu tasowa da su kara zurfafa hadin gwiwarsu karkashin dandalin hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta South-South cooperation, sannan su yi kokarin tantance hakikanin koma bayan ci gaba da suke fuskanta, inda ya bukaci a samar da karin muhimman taimako daga kungiyoyin bunkasa ci gaba na gamayyar kasa da kasa. (Ahmad)