logo

HAUSA

Rasha ta gudanar da faretin tunawa da ranar samun nasara kan dakarun Nazi

2022-05-10 10:15:03 CMG HAUSA

 

Rundunar sojojin kasar Rasha ta gudanar da gagarumin faretin soja a jiya Litinin a filin Red Square dake tsakiyar birnin Moscow, a wani bangare na tunawa da cika shekaru 77 da murkushe dakarun Nazi na kasar Jamus. Bikin dai na da nufin jinjinawa gudummawar kishin kasa da sojoji ’yan mazan jiya suka bayar ga tsohuwar tarayyar Soviet.

Gabanin gudanar da faretin na shekara shekara, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya gabatar da jawabi ga sojojin kasar sa, yana mai cewa, "Nauyi ne a kanmu mu wanzar da tunawa da wadanda suka murkushe dakarun Nazi, suka kuma gadar mana da aikin sanya ido, da tabbatar da cewa ba mu sake karo da mummunan yanayin yakin duniya ba a nan gaba".

Shugaba Putin ya kara da cewa, har kullum kasarsa na yayata bukatar wani dunkulallen tsarin samar da tsaro, wanda zai yiwa daukacin sassan duniya amfani.

Daga nan sai ya yi tir da wasu kasashen yamma, bisa yadda suka jirkita tarihin yakin duniya na II. Yana mai cewa, Rasha na martaba daukacin sojojin hadin gwiwa, wadanda suka yi nasarar murkushe dakarun Nazi, da kuma manufar danniya ta soji.

Kusan sojoji 11,000 karkashin tawagogi 33 ne suka yi maci a filin Red Square, kafin kuma jerin gwanon makaman zamani, da sauran nau’ikan na’urorin ayyukan soji 131 su biyo baya.

A bana an gudanar da faretin sojin a biranen Rasha 28, a matsayin martaba gudummawar ’yan mazan jiya, yayin yakin kishin kasa na dakile dakarun Nazi na kasar Jamus, yakin da ya gudana tsakanin shekarun 1941 zuwa 1945, wanda muhimmin bangare ne na yakin duniya na II.

A yayin yakin, tsohuwar tarayyar Soviet ta rasa rayukan mutane kusan miliyan 27, wadanda suka hada da sojoji da fararen hula, kamar dai yadda alkaluman kididdigar hukumomin kasar suka tabbatar. (Saminu Hassan)