logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na Cambodia

2022-05-09 13:28:45 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira ga duniya da ta kara sauraron muryoyin nahiyar Asiya, yayin da tsarin shugabancin duniyar ke shiga zamanin Asiya.

Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da mataimakin firaministan Cambodia, kana ministan harkokin wajen kasar Prak Sokhonn ta kafar bidiyo.

A cewar Wang Yi, daga wata mai zuwa, Sin da Cambodia da Indonesia da Thailand, za su karbi bakuncin tarukan da suka hada da taron shugabannin kungiyar BRICS da na shugbannin kasashen gabashin Asia da na shugabannin kungiyar G20 da kuma na kungiyar APEC. Yana mai cewa, wannan zamani ne na Asiya wajen jagorantar shugabancin duniya, kuma kasa da kasa na sa ran Asiyar za ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

Ya jaddada cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da kasashen 3 wajen aikewa da sako mai karfi  game da kudurin Asiya na inganta zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da daukaka huldar kasa da kasa da kuma bada gudunmawa wajen shawo kan kalubalen da duniyar ke fuskanta. Har ila yau, ya ce kasar Sin ta yi imanin cewa, ya kamata duniya ta kara sauraron muryar nahiyar Asiya da girmama matsayarta da kuma amfana daga basirarta. (Fa’iza Mustapha)