logo

HAUSA

Amurka ba ta da iznin zargin jama’ar Afirka kan zabin yin hadin gwiwa tare da Sin

2022-05-09 20:38:22 CMG Hausa

A yayin ziyarar da mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Amurka Wendy Sherman ta yi a nahiyar Afirka, ta bayyana cewa, wasu kasashen Afirka sun zabi kamfanin Huawei na kasar Sin a matsayin kamfanin dake samar da hidimar sadarwa, wai wadannan kasashe sun yi watsi da ikon mulkin kasa. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, zargin da jami’ar Amurka ta yi kan kasar Sin ba shi da tushe. Ya rage ga kasashen Afirka da jama'ar su zabi wadanda za su yi hadin gwiwa da su, kuma ba Amurka ba ce ta yanke hukunci.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, ra’ayin madam Sherman ta shaida yunkurinta na kin kasar Sin da tada rikici a tsakanin Sin da Afirka. Kamfanonin Sin ciki har da kamfanin Huawei suna gudanar da hadin gwiwa mai kyau tare da kasashen Afirka da ma sauran kasashen duniya da dama, wanda ta sa kaimi ga kyautata da bunkasa ababen more rayuwar jama’a ta aikin sadarwa, da samar wa mazauna wurin hidimar sadarwa ta zamani mai inganci da tsaro da kuma araha, wanda ta samu karbuwa sosai a wajen jama’a. A yayin da ake yin hadin gwiwar, ba a samu wata matsala ta batun leken asiri ko kawo illa ga tsaron yanar gizo ko daya ba. (Zainab)