logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz Ta Kafar Bidiyo

2022-05-09 21:36:24 CMG HAUSA

A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ta kafar bidiyo.

Yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashe Sin da Jamus musamman suna bukatar ci gaba da kyautata huldar dake tsakanin su cikin lumana da kwanciyar hankali, da ba da cikakkiyar gudummawa wajen tabbatar da daidaito mai inganci, da jagorancin dangantakar dake tsakanin kasashe biyu, wanda ba kawai zai amfanar da kasashen biyu da jama’arsu ba, har ma zai ba da gudummawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Scholz ya ce, a shirye bangaren Jamus yake ya yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, da yin cudanya da juna a dukkan matakai, da gudanar da wani sabon zagaye na shawarwarin gwamnatocin Jamus da Sin, da karfafa yin hadin gwiwa a fannonin kasuwanci da zuba jari, da batun sauyin yanayi, da yaki da annoba, da harkar kiwon lafiya, da ilmi da al'adu.

Dangane da halin da ake ciki a kasar Ukraine kuwa, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, rikicin kasar Ukraine ya sake jefa tsaron kasashen Turai cikin wani mawuyacin hali. Don haka, ya kamata bangaren Turai ya nuna alhakinsa na tarihi da hikimar siyasa, ya yi tunani game da zaman lafiyar Turai na dogon lokaci, da kuma neman warware matsalar ta hanyar da ta dace. Ya kamata tsaron Turai ya kasance a hannun al’ummar Turai da kansu. (Ibrahim)