logo

HAUSA

Kamfanin sarrafa karafa na Sin ya daddale yarjejeniyar hakar ma’adinan karfe a Kamaru

2022-05-08 19:14:14 CMG Hausa

Reshen kamfanin sarrafa karafa na kasar Sin dake kasar Kamaru da ma’aikatar kula da hakar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi ta kasar Kamaru sun daddale yarjejeniyar hakar ma’adinan karfe a kasar Kamaru da jarin da aka zuba a fannin wanda ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 700.

Ministan kula da hakar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi na kasar Kamaru Gabriel Dodo Ndoke, da manajan reshen kamfanin Zheng Zhenghao sun daddale yarjejeniyar.

Bisa bayanin da kamfanin sarrafa karafa na kasar Sin ya yi, yarjejeniyar ta hada da aikin hakar ma’adinan karfe dake birnin Kribi na kudancin kasar Kamaru. Bayan da aka fara aikin, ana sa ran, nauyin karfe da ake tacewa da kashi 60 cikin dari a shekara daya zai kai ton miliyan 4.

Minista Dodo ya bayyana cewa, wannan aiki zai sa kaimi ga samun moriyar tattalin arziki da kuma bunkasuwa mai dorewa. A matsayin wani kamfanin dake aiwatar da ayyukansa a kasa da kasa, kamfanin sarrafa karafa na kasar Sin yana da fasahohi da kudi, ya samar da kyakkyawar dama ga kasar Kamaru wajen samun bunkasuwa.

A nasa bangare, Zheng Zhenghao ya bayyana cewa, aikin hakar ma’adinan karfe zai sa kaimi ga kasar Kamaru na samu kudin shiga, kana zai samar da ayyukan yi ga mutane kimanin 600 a kasar kai tsaye. (Zainab)