logo

HAUSA

Xi Jinping da Mahaifiyarsa

2022-05-08 15:23:11 CMG Hausa

A kan kantar littattafai ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, ana iya ganin wannan hoto.

Xi na nuna biyayya sosai ga mahaifiyarsa. Idan ba ya shan aiki, ya kan yawata tare da ita rike da hannunta, yana hira da ita, bayan sun ci abinci tare.

Shugaba Xi Jinping na nuna biyayya ga iyayensa da kaunar iyalansa sosai, kamar yadda ake yi kullum.

Yayin da Shugaba Xi yake karamin yaro, wato kusan shekaru biyar ko shida da haihuwa, mahaifiyarsa ta goye shi a bayanta, sun je wani dakin sayar da litattafai domin sayen littafin da aka rubuta kan labarin Yue Fei, shahararren jarumin daular Song ta kudu ta kasar Sin, inda ta gaya masa cewa, mahaifiyar Yue Fei, ta taba sassaka kalmomi guda hudu masu ma'anar "Bautawa kasa" a bayan jikinsa, har yanzu shugaba Xi bai manta da kalmomin nan hudu ba, har ma ya mayar da su a matsayin burinsa na tsawon rai.

Xi ya taba bayyana cewa, "Ya dace iyaye su koyar da yaransu tunanin da'a, da hali na gari tun suna kanana, da haka ne yaran za su girma cikin koshin lafiya, har su ba da gudummowa ga ci gaban kasa."

Tabbas shugaba Xi ya koyi halin bautawa kasa da jama'a daga iyalinsa.

Har kullum shugaba Xi yana maida hankali kan iyali, haka kuma yana kaunar iyalinsa matuka, amma yana shan aiki a ko da yaushe, ta yadda ba ya iya haduwa da iyalinsa ko a lokacin hutu.

Yayin bikin bazara na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na shekarar 2001, mahaifiyarsa Qi Xin ta taba buga waya ga Xi, wanda shi ne shugaban jihar Fujian a wancan lokaci, inda ta gaya masa cewa, "Muddin dai ka gudanar da aiki cikin lumana, to mun gamsu sosai, saboda idan ka dukufa kan aiki, za ka sauke nauyin dake wuyanka, babu bambanci."

Babu bambanci tsakanin "karamin gida" da "babban gida", wato iyali da kasa, mahaifiyarsa tana fadawa danta ya sauke nauyin raya kasa dake bisa wuyansa, saboda ta fahimce shi, kuma tana goyon bayansa.

A don haka, shugaba Xi ya mayar da nufin samar da wadata ga daukacin iyalan kasar Sin a matsayin muradunsa.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, shugaba Xi bai taba mantawa da abun da mahaifiyarsa ta koyar da shi ba, yana dukufa kan aikin bautawa kasa da jama'a.(Kande Gao)