logo

HAUSA

Sama da mutane 16,000 ne suka mutu sanadiyyar ayyukan masu tsatssauran ra’ayi a yammacin Afrika cikin shekaru 3

2022-05-06 10:44:05 CMG Hausa

Kungiyar ECOWAS, mai raya tattalin arzikin yammacin Afrika, ta ce a kalla mutane 16,726 ne suka mutu sanadiyyar rikicin masu tsatssauran ra’ayi a yammacin Afrika, cikin shekaru 3 da suka gabata.

Dominic Nitiwul, ministan tsaron kasar Ghana ne ya bayyana haka a jiya, yayin wani taron yini biyu na manyan hafsoshin tsaron kasashen kungiyar ECOWAS a birnin Accra.

A cewarsa, cikin shekaru 3 da suka gabata, an kai hare-haren ta’addanci har sau 5,306 a yankin, wadanda suka yi sanadin asarar rayuka sama da 16,726, baya ga dubban mutanen da suka jikkata da wasu miliyoyi da suka rasa matsugunansu.

Dominic Nitwul ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro su samar da yanayin da ya dace na hadin gwiwa a tsakaninsu domin kara musayar bayanan sirri da za su kai ga bibiyar ayyukan kungiyoyin ’yan ta’adda da sauran masu dauke da makamai, wadanda su ma ke musayar bayanai tsakanin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)