logo

HAUSA

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da fashewar wani bam a cibiyar mai inda ake fargabar mutane biyu sun mutu

2022-05-05 10:42:35 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya jiya Laraba, ta tabbatar da fashewar wani bam a wata cibiyar mai a jihar Imo da ke kudancin kasar, inda ake fargabar a kalla mutane biyu sun gamu da ajalinsu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar ta Imo Mike Abattam, ya shaidawa manema labarai a Owerri, babban birnin jihar cewa, fashewar ta afku ne da sanyin safiyar jiya Laraba, a wani katafaren kamfanin mai da ke garin Izombe na karamar hukumar Oguta a jihar ta Imo.

Abattam ya ce, ’yan sanda sun fara gudanar da bincike kan musabbabin fashewar bam din, da ake zargin wasu ’yan kunar bakin wake biyu ne suka haddasa. Yanzu haka, an tura jami’an ’yan sanda yankin, domin hana tabarbarewar doka da oda.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito ma’aikatan wurin na cewa, an kashe mutane biyun da ake zargin ’yan kunar bakin wake ne, a yayin da bam din ya tashi a lokacin da suke kokarin shiga tashar ta kofar shiga. (Ibrahim)