logo

HAUSA

Shugaban Jamus: Jamus ta riga ta rage dogaro da makamashi daga Rasha

2022-05-05 15:47:30 CMG Hausa

Shugaban Jamus Frank Walter Steinmeier ya bayyana a Bucharest, babban birnin Romania cewa, Jamus ta rage dogaro da Rasha wajen samun makamashi.       

A wannan rana, Frank Walter Steinmeier ya ziyarci Romania, inda ya tattauna da takwaransa na Romania Klaus Iohannis kan yanayin da ake ciki a Ukraine da tsaron gabashin NATO da takunkuman da kungiyar EU ta kakaba wa Rasha da dai sauransu. A yayin taron ’yan jarida da aka gudanar bayan tattaunawar, Frank Walter Steinmeier ya ce, Jamus ta rage dogaro da makamashin Rasha matuka, kana yawan man da take shigowa daga Rasha ya ragu zuwa kashi 15 cikin kashi 100.              

Klaus Iohannis ya ce, nuna goyon baya ga Ukraine yana da muhimmanci matuka, kuma Romania za ta taimakawa Ukraine fitar da kayayyaki gami da abinci zuwa kasuwa na uku. Romania na son taka rawar gani wajen cimma manufa mai muhimmanci na raba iskar gas ga kungiyar EU. (Safiya Ma)