logo

HAUSA

An ba da rahoton mutane 274 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Shanghai

2022-05-03 15:51:30 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta birnin Shanghai na kasar Sin, ta ba da rahoton mutane 274 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a cikin gida, da kuma wasu mutane 5,395 da ba su nuna alamomin cutar ba a jiya Litinin.

Mahukuntan birnin sun yi rajistar mutane 20 da suka mutu sanadiyar COVID-19 a ranar Litinin, dake da matsakaicin shekaru 83.95. Dukkan wadanda suka mutu dai suna da matsalolin lafiya masu tsanani, da suka hada da sankarar mafitsara, da ciwon zuciya mai tsanani da cututtuka masu nasaba da zuciya.

A cewar wani taron manema labarai kan matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar, a halin yanzu dai, sama da rabin mazauna birnin Shanghai, suna zaune ne a cikin “yankuna marasa hadari da aka takaita matakan yaki da cutar”, bisa ga sabbin gyare-gyaren da birnin ya yi, na rarraba yankuna mafiya hadarin COVID-19 kashi uku,

Ya zuwa ranar Litinin, adadin mutanen da ke "yankunan rigakafin cutar," yankunan da ba a ba da rahoton kamuwa da cutar ba a cikin kwanaki 14 da suka gabata, ya haura miliyan 15.47.

A halin yanzu, adadin mutanen da ke cikin "yankunan da aka hana kai koma a cikinsu," yankunan da ba a ba da rahoton kamuwa da cuta ba a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, ya kai mutane miliyan 5.38. Adadin mutanen da ke zaune a cikin "wuraren da aka killace," inda aka ba da rahoton kamuwa da cuta a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, ya kai miliyan 2.54.(Ibrahim)