logo

HAUSA

Sin ta fara gwajin rigakafi nau’in Omicron ga jikin dan adam

2022-05-02 20:16:01 CMG Hausa

A ranar Lahadin nan kasar Sin ta kaddamar da gwajin rigakafin cutar COVID-19 nau’in Omicron ga jikin dan adam a birnin Hangzhou dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.

Rukunin nazarin halittu na kasar, wani karamin sashe na kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinopharm, shi ne ya samar da rigakafin, wanda har yanzu ake ci gaban da aikin bincike kansa, kuma an fara gwajin ne tun a watan Disambar shekarar 2021, a cewar kamfanin.(Ahmad)