logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin a Saliyo ya baiwa musulmi kyautar kayan abinci

2022-04-29 10:55:00 CMG HAUSA

 

Ofishin jakadancin Sin dake kasar Saliyo ya mika kyautar kayayyakin abinci ga al’ummar musulmi, albarkacin watan azumin Ramadan, da kuma bikin cikar kasar shekaru 61 da samun ’yancin kai, wanda ya fado ranar Laraba.

Yayin mika kayan tallafin a jiya Alhamis a birnin Freetown, fadar mulkin kasar, jakadan Sin a Saliyo Hu Zhangliang ya ce, kayayyakin sun kunshi shinkafa, da man girki, da fulawa, da sikari. Ya kara da cewa, "Ina mika sakon murna ga shugaba Julius Maada Bio, da gwamnatin Saliyo, da daukacin al’ummar kasar, don gane da kokarinsu wajen bunkasa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban daban.” Ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar game da kyautatawa rayuwar mabiya addinin musulunci da ke kasar.

Hu ya kara da cewa, ko shakka babu al’ummar musulmin Saliyo ta yi rawar gani, wajen yaukaka kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Saliyo, don haka yake fatan ta hannun wadanda aka damkawa kayayyakin, tallafin zai isa ga mabukata cikin al’ummar kasar.

Da yake bayyana godiya a madadin gwamnatin Saliyo, ministan ma’aikatar walwala da jin dadin jama’a Bendu Dassama, ya jinjinawa ofishin jakadancin na Sin. Yana mai cewa tallafin ya zo a daidai gabar da ake bukatarsa, kamar yadda kasar Sin ta saba yi a ko da yaushe. (Saminu)