logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Fara Aiwatar Da Sabuwar Dokar Ba Da Ilmin Sana’a Daga Ranar 1 Ga Watan Mayu

2022-04-28 11:52:24 CMG HAUSA

 

Hukumar ba da ilmi ta kasar Sin, ta kira taron manema labarai a jiya Laraba, inda ta yi bayani game da gyaran da aka yi wa dokar ba da ilmin sana’a. 

Daga ran 20 ga watan, zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na 13, ya zartas da sabuwar dokar da aka yiwa gyaran fuska, kuma za a gabatar da ita a ran 1 ga wata mai zuwa. 

Hanya mafi dacewa wajen kara muhimmancin ba da ilmin sana’o’i ita ce daga matsayinsa, da samar da guraben aikin yi a fannin. Sabuwar dokar za ta mai da hankali kan matsalolin da masu kammala karatu daga wadannan makarantu suke fuskanta, don su samu ci gaba a nan gaba.

Sabuwar dokar ta yi tanadin cewa, kamfanoni ba za su iya nuna bambancin ra’ayi kan daliban da za su kammala karatunsu daga makarantar koyon ilmin sana’o’i ba, ya kamata su samar musu yanayin adalci wajen yin takara da daliban jami’o’i. Matakan da za su baiwa wadannan dalibai tabbaci wajen amfani da kwarewarsu yadda ya kamata, da kare moriyarsu daga fannoni daban-daban, ta hakan za a bunkasa aikin samar da ilmin sana’o’i yadda ya kamata. (Amina Xu)