logo

HAUSA

AfCFTA za ta bunkasa sashen masana’antun sarrafa magunguna na Afirka

2022-04-28 10:56:54 CMG HAUSA

 

A jiya Laraba ne, mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya da masana’antu a Ghana Michael Okyere Baafi, ya bayyana yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA, a matsayin wata babbar dama ta bunkasa sashen masana’antun sarrafa magunguna na nahiyar Afirka.

Mr. Baafi, wanda ya furta hakan yayin da yake kaddamar da bikin baje kolin hajojin magunguna, da na kiwon lafiya mai lakabin WAPHC, ya ja hankalin masana’antun da lamarin ya shafa, da su yi amfani da damammakin dake kunshe cikin yarjejeniyar ta AfCFTA, wajen fadada ayyukansu, ta yadda Afirka za ta shiga a dama da ita a fannin takara, da cin riba a wannan fanni.

Daga nan sai ministan ya bayyana burin gwamnatin Ghana na daga matsayin kamfanonin sarrafa magunguna dake kasar, ta yadda za su kai matsayin inganci da hukumar WHO ta aminta da shi, tare da samun damar shiga kasuwannin cikin nahiyar Afirka, da ma na duniya baki daya.

A nasa bangare, shugaban kamfanin AGI Mr. Seth Twum Akwaboah, ya ce bayan fara amfani da yarjejeniyar ta AfCFTA, akwai bukatar masana’antun dake nahiyar Afirka da su maida hankali ga yin takara tsakanin su, da nufin ko dai fitar da hajojin su waje, ko sayar da su a gida.  (Saminu)