logo

HAUSA

Duniya na jiran amsa daga “mai ikirarin kare hakkin bil'adama”

2022-04-27 21:17:24 CMG Hausa

A baya-bayan nan, kwararru kan kare hakkin dan Adam masu zaman kansu guda 14 na Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka bukaci gwamnatin Amurka da ta dawo da kadarorin biliyoyin daloli mallakar babban bankin kasar Afghanistan.

Biliyoyin daloli za su iya ceton rayuwar al’ummar duk kasar Afghanistan. Alkaluman kididdigar da hukumomin kasa da kasa suka fitar sun nuna cewa, sama da mutane miliyan 23 a Afghanistan na bukatar agajin abinci cikin gaggawa. Bugu da kari, sama da 'yan Afghanistan miliyan 4 ne suka rasa matsugunansu.

Shin alhakin wane ne? Ko shakka babu Amurka ce. A shekara ta 2001, Amurka ta kaddamar da yaki a Afghanistan bisa dalilin wai "yaki da ta'addanci". Yakin na tsawon shekaru 20, ya yi sanadin mutuwar fararen hula ‘yan Afghanistan 100,000, kuma kusan miliyan 11 sun zama 'yan gudun hijira.

A watan Agustan shekarar da ta gabata, a kokarin da take yi na daidaita manyan tsare-tsarenta a duniya, Amurka ta yi gaggawar janye sojojinta daga Afghanistan. A watan Fabrairun wannan shekara, shugaban Amurka ya sanya hannu kan wata doka, da nufin raba kusan dala biliyan 7 na kadarorin Babban Bankin Afghanistan da Amurka ta kwace zuwa gida biyu, za a yi amfani da kashi 1 don biyan diyya ga wadanda suka yi hasara a lamarin ranar 11 ga watan Satumba ko kuma harin "9.11".

Ban da wannan kuma, a matsayinta na babbar mai haddasa rikicin Ukraine, Amurka ta amince da samar wa Ukraine rukunonin makamai guda takwas, jimillar taimakon soji da ta samar ta kai dalar Amurka biliyan 3.7. Kwace kudi daga Ukraine, raunana Rasha, lalata Turai, wadatar da masana’antun sojinta... Duk wadannan su ne ainihin abin da Amurka take so.

Duniya na jiran Amurka "mai ikirarin kare hakkin bil'adama", ta mayar da martani ga sukar da kwararrun kare hakkin bil'adama na MDD suka yi cikin hadin gwiwa. (Mai fassara: Bilkisu)