logo

HAUSA

AfDB: Farashin Alkama zai tashi da kaso 60 bisa dari a kasashen Afirka sakamakon rikicin Rasha da Ukraine

2022-04-27 14:14:16 CMG Hausa

Shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwunmi Adesina, ya ce rikicin Rasha da Ukraine, zai haddasa hauhawar farashin alkama da kusan kaso 60 bisa dari a kasashen nahiyar Afirka.

Akinwunmi Adesina ya bayyana hakan ne jiya Talata lokacin da yake zantawa da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, a fadar gwamnatin kasar dake birnin Abuja. Adesina ya shaidawa shugaba Buhari cewa, tashin hankalin ya haifarwa duniya tarin kalubale, musamman ma kasashen Afirka, masu shigo da kaso mai yawa na abincin da suke bukata daga kasashen biyu.

Adesina wanda tsohon ministan ma’aikatar noma ne a Najeriya, ya ce a daminar bana, bankin AfDB zai taimakawa kananan manoman Najeriya  a kalla miliyan 5, ta yadda za su iya noman hekta miliyan 1 ta masara, da hekta miliyan 1 ta shinkafa, da hekta 250,000 ta dawa da waken soya.

A nasa tsokaci, shugaba Buhari ya jinjinawa shirin bankin na AfDB, bisa kokarinsa na dakile duk wani mummunan tasiri da rikicin Rasha da Ukraine ka iya haifarwa, ta fuskar samar da isasshen hatsi. (Saminu)