logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin kare ikon mallakar fasaha na kamfanoni masu jarin waje

2022-04-27 11:26:49 CMG Hausa

A kwanan baya, an gabatar da rahoto game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin kare ikon mallakar kadarorin ilimi, da inganta muhallin kasuwanci cikin shekarar 2021, wanda ya nuna cewa, a bara, ’yan kasashen waje sun samu izinin mallakar fasahohi dubu 110 a kasar Sin, jimillar da ta karu da kashi 23% bisa ta shekarar 2020. Kana yawan tamburan da kamfanonin ketare suka yi rajistarsu a bara, ya kai dubu 194, adadin da ya karu da kashi 5.2% bisa na shekarar 2020.

Rahoton ya kuma nuna cewa, cikin shekaru 2 da suka wuce, kasar Sin ta kare matsayinta na daya daga cikin kasashe 10 da suka fi samun ci gaba ta fuskar kyautata muhallin kasuwanci.

A nasa bangare, kwamitin raya ayyukan ciniki tsakanin kasashen Amurka da Sin, ya gabatar da wani rahoto kan ingancin muhallin kasuwanci na kasar Sin cikin shekarar 2021, wanda ya shaida cewa, kashi 95% na kamfanonin da aka gudanar da bincike a kansu, suna samun riba a kai a kai, yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasar Sin.

Kaza lika kashi 74% na kamfanonin na kallon kasar Sin a matsayin kasuwa mafi muhimmanci, ko kuma daya daga cikin manyan kasuwanni 5 mafiya muhimmanci a duniya, inda suka zuba jari. (Bello Wang)