logo

HAUSA

Shaguna a Beijing sun dukufa wajen biyan bukatun al’umma yayin da adadin masu harbuwa da COVID-19 ke karuwa

2022-04-26 10:14:02 CMG HAUSA

 

Shaguna a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin na kara dukufa wajen tabbatar da ganin sun biya bukatun al’umma mazauna birnin, a gabar da adadin masu harbuwa da cutar COVID-19 ke karuwa, ake kuma hasashen shiga yanayi na tsaurara matakan dakile bazuwar ta a birnin.

Rahotanni na cewa, gundumar Chaoyang dake gabashin birnin na Beijing na kan gaba a adadin sabbin masu harbuwa da cutar. Mahukuntan birnin Beijing sun ba da umarnin gudanar da gwajin cutar ga daukacin mazauna, da masu aiki a gundumar Chaoyang, tare da tsarin sanya ido kan wasu yankunan gundumar don tabbatar da dakile bazuwar annobar zuwa karin sassa. (Saminu)