logo

HAUSA

An fadada gwajin COVID-19 zuwa karin sassan birnin Beijing

2022-04-26 10:14:28 CMG HAUSA

 

Za a gudanar da zagaye 3 na gwajin cutar COVID-19 a sassan birnin Beijing 11, tsakanin ranekun Talata zuwa Asabar mai zuwa, a wani mataki na dakile bazuwar cutar.

A yayin taron manema labarai na ranar Litinin, mahukuntan birnin sun ce tsakanin karfe 4 na yammacin Lahadi zuwa 4 na yammacin ranar Litinin, adadin sabbin wadanda suka harbu da cutar a birnin ya kai mutum 29.

A cewar Pang Xinghuo, mataimakiyar shugaban cibiyar kandagarkin cututtuka ta birnin Beijing, daga ranar Juma’a zuwa yanzu, an samu sabbin masu harbuwa da cutar 70 a birnin.  (Saminu)