logo

HAUSA

Babu wanda ke son yakin duniya na uku

2022-04-26 19:24:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Talatar nan cewa, babu wanda yake son ganin barkewar yakin duniya na uku, kuma kasar Sin tana goyon bayan warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar diflomasiyya.

Wang ya ce, ya kamata dukkan bangarorin su fara goyon bayan tattaunawa da yin shawarwari don hana rikicin ya kara ta’azzara, ta yadda Turai da ma duniya za su kaucewa fuskantar mummunan sakamako.