logo

HAUSA

Hukumomin agaji sun bukaci a gaggauta samar da kudade don magance karancin abinci a gabashin Afrika

2022-04-26 10:56:39 CMG HAUSA

 

Sama da hukumomin agaji 50 ne suka bukaci a gaggauta samar da karin kudade da samar da kyakkyawan jagoranci don tinkarar gagarumar matsalar ayyukan jin kai dake fuskantar miliyoyin mutanen shiyyar gabashin Afrika a sanadiyyar matsanancin fari, inda aka yi gargadin cewa, muddin aka yi jinkiri za a iya samun hasarar rayuka.

Hukumomin da suka hada da kungiyar agaji ta Save the Children, da Norwegian Refugee Council, da gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu  a Somaliya, sun bayyana hakan cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, gabanin babban taron kungiyoyin bada tallafi na kasa da kasa da za a gudanar a yau Talata a Geneva. An bayyana cewa, sama da mutane miliyan 14 ne a kasashen Somaliya, da Habasha da Kenya, kuma kusan rabin adadin kananan yara ne, sun riga sun fada yanayin tsananin yunwa.

Kurt Tjossem, mataimakin shugaban shiyyar na kwamitin ayyukan ceto na kasa da kasa IRC, ya bayyana cewa, ba zai yiwu a sake maimaita kuskuren da aka yi a baya ba, kuma aka kau da kai kan batun har sai da lokaci ya kure. Yanzu ne lokacin da ya dace a dauki matakai, domin kaucewa fadawar miliyoyin mutanen shiyyar gabashin Afrika cikin garari.

Tjossem ya ce, matsalolin tashe-tashen hankula, da rashin tsaro, da karayar tattalin arziki, sun kara kamari a shekaru da dama, a yanzu kuma, ga batun matsalar sauyin yanayi, da kauracewar dunbun al’umma daga muhallansu lamarin dake kara sanadaiyyar fadawar karin mutane cikin yanayin tsananin bukata. (Ahmad)