logo

HAUSA

Xi Jinping ya ziyarci jami'a, don karfafawa matasan Sin gwiwar cika burin farfado da kasa

2022-04-25 21:46:29 CMG Hausa

A gabannin ranar 4 ga watan Mayu, wato ranar matasan kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a jami'ar Renmin ta kasar Sin a yau Litinin, don taya matasan kabilu daban daban na kasar murnar bikin. Ya kuma bayyana fatansa na ganin matasan kasar, su kuduri aniyar farfado da kasa, da kokarin cimma kyakkyawan sakamako a matsayinsu na matasa na zamani.

Xi Jinping ya shiga cikin ajujuwan siyasa da ake amfani da na’urori masu kwakwalwa wajen gudanar da su, da dakin adana kayayyakin tarihi, da dakunan karatu. Ya kuma kara fahimtar yadda jami’ar take kokarin yin gyare-gyaren dabarun koyar da darussan siyasa, da tarihin jami’ar, da nasarorin da aka samu daga aikin koyarwa, da kara kare da kuma amfani da tsofaffin adabi da littattafan tarihi, da ma yadda jami’ar take amfani da sakamakon bincike zuwa abubuwa a zahiri da dai sauransu.

A yayin taron kara wa juna sani da wakilan malamai da dalibai, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana da tarihi da al'adu da kuma yanayin kasa na musamman, saboda haka, a yayin da ake gina jami'a mai salon musamman na kasar Sin, kuma mai daraja a duniya, bai kamata a yi koyi da wasu ba, a maimakon haka dole ne a nemo wata sabuwar hanya. Sana’ar ba da ilmi sana’a ce dake bukatar daukar nauyi sakamakon nuna kauna. Ya kamata malamai su rika nuna kauna ga kowane dalibi, domin su samu damar haskakawa a rayuwarsu.