logo

HAUSA

Kwayar maganin artemisinin ta ba da babbar gudummawa ga kawar da cutar malariya a duniya

2022-04-25 20:35:43 CMG Hausa

Yau 25 ga watan Afrilu, rana ce ta yaki da cutar malariya ta kasa da kasa, kuma shekarar da muke ciki ta zo daidai da cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin malariya ta Artemisinin. A matsayin ta na muhimmiyar alama da kasuwanci na kasar Sin wajen taimakawa rigakafin cutar malariya, artemisinin ya ba da gudummawa sosai ga rigakafin cutar a duniya baki daya.

Bayanai na nuna cewa, a cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa wajen shawo kan cutar malariya, ta hanyar samar musu da maganin artemisinin, da horar da ma'aikata, da tura kwararrun likitoci, da gina cibiyoyin yaki da cutar da dai sauransu. A yankin kudu da hamadar sahara kadai, akwai mutane kimanin miliyan 240 da suka ci gajiyar amfani da maganin artemisinin.

A kasar Comoros, wadda ta taba fama da cutar malariya, ta yi nasarar rage mace mace sakamakon kamuwa da cutar malariya bisa taimakon kwayar maganin artemisinin da ma'aikatan agaji na kasar Sin.

Game da haka, shugaban kasar Comoros Azali Assoumani ya ce, wannan ya biyo bayan hangen nesa na masu bincike na kasar Sin da kuma babban tallafin da wannan babbar kasar ta gari ta ba mu. Tun daga shekara ta 2007 zuwa yanzu, mun sami nasarar kawar da fiye da kaso 80 cikin 100 na cutar malariya tsakanin al'ummar kasar, tare da rage yawan kamuwa da cutar da fiye da kashi 90 cikin 100 sakamakon yadda aka yi amfani da sinadarin artemisinin cikin hanzari wajen kawar da cutar malariya da kuma amfani da maganin don rigakafi da kawar da cutar a tsakanin dukkan al’ummar kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)