logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa yayin da tsarin cudanyar sassan kasa da kasa ke fuskantar barazana

2022-04-25 10:51:30 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su kara hada kai da juna, domin tabbatar da karfafa hadin gwiwar kasashen duniya, a gabar da cudanyar kasa da kasa ke fuskantar babban kalubale.

Mr. Guterres ya yi wannan kira ne cikin sakonsa na ranar kasa da kasa ta cudanyar dukkanin sassa da diflomasiyya don zaman lafiya, wadda ake gudanarwa duk shekara a ranar 24 ga watan nan na Afirilu.

Jami’in ya ce kasashe mambobin MDD sun rattaba hannu, ko sun amince da dokar MDD mai nasaba da wannan batu, sun kuma himmatu wajen kare manufar cudanyar dukkanin sassa, da raya diflomasiyya domin wanzar da zaman lafiya. To sai dai kuma wannan manufa na fuskantar babban kalubale ta bangarori daban daban, ciki har da mummunan tasirin sauyin yanayi, da kuma yawaitar tashe-tashen hankula.

Guterres ya ce, “Akwai bukatar sauya wannan yanayi. A rana irin ta bikin kasa da kasa na cudanyar dukkanin sassa, da diflomasiyya don zaman lafiya, ina kira ga dukkanin gwamnatoci, da shugabanni, da su sake azama wajen gudanar da shawarwari, tare da zakulo dabarun shawo kan kalubalolin dake addabar duniya, wadanda za su wanzar da hanyar zaman lafiya". (Saminu)