logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu tsoffin farfesoshin jami'ar kimiyya da fasaha ta Beijing suka aika masa

2022-04-22 15:39:42 CMG Hausa

 

Jiya ne, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, shugaban kasar, ya amsa wasikar da wasu tsoffin farfesoshi na jami'ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing suka rubuta masa, inda ya kara dagewa wajen zakulo hazakai masu inanci, da inganta ci gaban masana'antun karafa, da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, tun bayan kafuwarta zuwa yanzu, jami'ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing ta ba da gudummawa mai kyau ga bunkasuwar masana'antun karafa ta kasar Sin. A yayin da ake bikin cika shekaru 70 da kafuwar jami'ar, Xi ya ce yana mika gaisuwa da kuma sakon taya murna da fatan alheri ga farfesoshi da dalibai, da ma'aikata, da tsofaffin daliban jami'ar. (Ibrahim)