logo

HAUSA

Yawan jarin kai tsaye da bai shafi kudi ba da kasar Sin ta zuba ya karu da kashi 6.3 a rubu’i na farko

2022-04-22 14:04:23 CMG Hausa

 

Wasu alkaluma da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar jiya Alhamis sun nuna cewa, jarin kai tsaye da kasar ta zuba wanda bai shafi harkokin kudi ba, ya kai kudin Sin yuan biliyan 170.95 a watannin ukun farko na shekara, karuwar kaso 6.3 bisa dari kan na shekarar bara.

Inda aka juya zuwa dalar Amurka kuwa, jarin na ODI ya karu da kashi 8.5 daga shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan 26.92,

A cikin rubu’i na farko, jarin kai tsaye da bai shafi harkokin kudi ba da kasar Sin ta zuba a cikin kasashen da ke kan hanyar shawarar ziri daya da hanya daya, ya karu da kashi 19 cikin dari bisa na shekarar bara zuwa dala biliyan 5.26.

Ma'aikatar ta kara da cewa, jarin na ODI da aka zuba a bangaren manyan hajoji da kayayyaki da ake sayarwa, ya karu da kashi 36.3 bisa dari a shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan 5.45, yayin da jarin da aka zuba a fannin masana'antu, ya karu da kashi 13.3 cikin dari. (Ibrahim)