logo

HAUSA

Zhao Lijian: Duniya na sane da kasar dake cin ribar rikicin Rasha da Ukraine

2022-04-22 20:05:58 CMG Hausa

A ranar Laraba ne hukumar MDD mai lura da ‘yan gudun hijira, ta bayyana cewa, sama da ‘yan kasar Ukraine miliyan 5 ne suka kwarara zuwa kasashen Turai makwafta, lamarin da ya haifar da gagarumar matsalar ‘yan gudun hijira.

To sai dai kuma, yayin da wasu sassan ke ganin nahiyar Turai ce mafi tafka asara, tun bayan barkewar rikicin Rasha da Ukraine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce tun bayan barkewar rikicin watanni 2 da suka gabata, a yanzu duniya na kara fahimtar bangaren da ke more riba, sakamakon rikicin.

Zhao wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya ce duk da Amurka na yiwa kan ta kirarin mai kare hakkokin bil adama, a hannu guda, ‘yan kasar Ukraine 12 ne kacal suka samu mafaka a Amurka cikin watan Maris da ya shude, karkashin shirin ta na baiwa ‘yan gudun hijira matsuguni.

Game da kalaman wasu ‘yan siyasar Amurka, na zargin kasar Sin da karya ka’ida kuwa, Zhao Lijian ya ce, babu wata kasa da ta kai Amurka kalubalanta, da kokarin lalata tsarin dokokin kasa da kasa, da ma duk wani tsari na cudanyar kasashen duniya. (Saminu)