logo

HAUSA

Mahalarta taron dandalin Boao sun yi kira ga kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwar yaki da cutar Covid-19

2022-04-22 15:51:49 CMG Hausa

Har zuwa yanzu, cutar Covid-19 na daya daga cikin kalubalolin da yan Adam ke fuskanta. A gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao da ke gudana, mahalarta taron sun ba da shawarwarinsu ta fannin rage gibin da ke tsakanin kasa da kasa ta fannin yaki da cutar, wadanda kuma suka yi nuni da cewa, kasar Sin na ba da babbar gudummawa ta wannan fanni.

Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, bayan da kasar Sin ta kirkiro rigakafin cutar, ya zuwa yanzu ta riga ta samar da alluran rigakafin sama da biliyan 2.1 ga kasashe da kungiyoyin duniya sama da 120, kuma ta raba fasahohinta ga kasashe sama da 20. Baki mahalarta taron sun amince da kokarin da kasar Sin take yi, ta fannin rage gibin da ke tsakanin kasa da kasa ta fannin shawo kan cutar.


Gargee Ghosh, babbar jami’ar kula da gidauniyar Bill & Melinda Gates, ta bayyana cewa, “Sakamakon kirkire-kirkiren da ake ta yi a kasar, da ma karuwar karfinta na samar da kayayyaki, da kuma karuwar alkawuran da aka dauka na hadin gwiwar kasa da kasa, kasar Sin ta riga ta zamanto kasar da ke taka muhimmiyar rawa, wajen rage gibin dake tsakanin kasa da kasa a bangaren shawo kan cutar Covid-19.”

A nasa jawabi, mataimakin shugaban hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, Mr. Deng Boqing ya ce, yawan rigakafin da kasar Sin ke iya samarwa a ketare ya kai biliyan daya a shekara, kuma kasar Sin tana son kara inganta hadin gwiwa da kasa da kasa, don ba da gudummawarta wajen saukaka gibin da ke tsakanin kasa da kasa ta fannin shawo kan cutar Covid-19.” (Lubabatu)