logo

HAUSA

Xi ya ba da shawarar inganta tsaro a duniya

2022-04-21 11:11:41 CMG HAUSA

 

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar matakan tabbatar da tsaro a duniya, a wani mataki na inganta tsaro ga kowa a fadin duniya.

Xi ya gabatar da shawara ce, yayin da yake gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, a lokacin bude taron shekara-shekara na taron dandalin Asiya na Boao na shekarar 2022.

Xi ya bayyana cewa, tsaro shi ne sharadi na samun ci gaba, kuma daukacin bil-Adama na rayuwa a cikin al'umma mai cikakken tsaro da ba za a iya raba su ba.

Shugaba Xi ya kara da cewa, an sha tabbatarwa a lokuta da dama cewa, babu abin da tunanin yakin cacar-baka zai haifar, illa lalata tsarin zaman lafiyar duniya kawai, kana mulkin kama karya da siyasar nuna iko, ba za su taba haifar da ‘da mai ido ba, sai ma illata zaman lafiyar duniya kawai, haka kuma yin fito na fito zai kara tsananta kalubalen tsaro ne kawai a karni na 21. (Ibrahim)