logo

HAUSA

Xi ya yi kira da zamar da Asiya mai jagorantar zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa a duniya

2022-04-21 11:19:25 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a zamar da Asiya nahiya mai jagorantar zaman lafiyar duniya, kuma jigon ci gaban duniyar, haka kuma abun misali ga hadin gwiwar kasa da kasa. Xi Jinping ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar ta bidiyo yayin bikin bude taron Boao na Asiya na 2022. A cewarsa, kamata ya yi nahiyar Asiya ta rike makomarta a hannunta.  (Fa’iza Mustapha)