logo

HAUSA

Wang Wenbin: Tattalin arzikin kasar Sin na cikin kyakkyawan yanayi

2022-04-19 20:29:24 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na da ingantaccen tsarin masana’antu, da babbar kasuwa mai faffadan muhalli ga kowa, tana kuma da tarin moriya da aka samu daga manufar gudanar da gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga waje.

Wang wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da yake amsa tambaya game da bunkasar tattalin arzikin kasar a rubu’i na daya na shekarar bana, ya kara da cewa, Sin na da tsarin jagorancin tattalin arziki mai inganci, wanda ke tasiri wajen dakile duk wani yanayi na hadurra da ake iya fuskanta. Kaza lika kasar ta cimma nasara wajen raya tattalin arziki mai yalwa da dorewa, lamarin dake kara ingiza nasarori, ga matakin farfadowar tattalin arzikin duniya.

A baya bayan nan, sashen harkokin wajen Amurka ya fitar da wani rahoto, game da kayyade makamai, wanda a ciki ya zargi kasar Sin da kin cika alkawuran ta, don gane da wannan batu.

Game da hakan, Wang Wenbin ya ce game da martaba dokokin kayyade makamai na kasa da kasa, al’ummun duniya na da ra’ayin su bisa shaidu na zahiri, game da yadda Sin da Amurka ke kiyaye dokokin ko akasin haka. (Saminu)