logo

HAUSA

Sin na fatan tashar binciken sararin samaniyarta za ta ingiza raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya

2022-04-18 11:50:18 CMG HAUSA

 

Ran 16 ga wata, bangaren dawowa na kumbon Shenzhou-13 na kasar Sin, ya sauka a doron duniya lami lafiya, kuma aikin kumbon ya kammala cikin nasara, abin da ya nuna cewa, Sin ta cimma nasarar aikin gwajin fasaharta a fannin tashar binciken sararin samaniya. Bisa shirin, kasar Sin za ta kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyarta a wannan shekarar da muke ciki, daga baya kuma za ta gudanar da ayyukan zirga-zirga sau 6. A halin yanzu, an zabi ‘yan saman jannati da za su yi aiki a kumbunan Shenzhou-14 da 15, inda ake ba su horo da aikin share fage yadda ya kamata.

Darektan ofishin aikin kumbon zirga-zirgar sararin samaniya dake dauke da ‘yan saman jannati na kasar Sin Hao Chun ya yi bayanin cewa, bayan an kammala aikin gina tashar a bana, tashar za ta shiga wani sabon mataki na aikace-aikace da bunkasuwa wadda za ta shafe fiye da shekaru 10.

Hao Chun ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin mu’ammala mai zurfi da hadin kai tare da kasashen duniya da suka kuduri aniyar amfani da sararin samaniya cikin lumana, bisa ka’idar daidaito da cin moriya da samun ci gaba tare. Ya ce:

“Muna fatan mai da tashar bincike sararin samaniya ta kasar Sin a matsayin wani dandalin dake ingiza raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, ta yadda ‘yan saman jannati da tawagogi masu binciken sararin samaniya na kasashe daban-daban, za su kara hadin kai wajen nazarin sararin samaniya, a kokarin amfanawa dukkan bil Adama.” (Amina Xu)