logo

HAUSA

Tunisia za ta dauki matakan magance gurbatar muhalli bayan kifewar jirgin ruwan dakon mai

2022-04-18 11:45:12 CMG Hausa

Shugaban kasar Tunisia, Kais Saied, ya bayar da umarni ga sojojin ruwan kasar da su dauki matakan magance mummunan tasirin gurbacewar muhalli a sakamakon kifewar jirgin ruwan dakon man fetur, don kandagarkin kaucewa fuskantar karin bala’u.

A wata sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa, za a yi amfani da dukkan damammakin da ake da su don tsarawa, da kuma tuntubar hukumomin da abin ya shafa, da kwamitocin shiyyoyin kasar, don tinkarar bala’in tare da daukar matakan hana tsiyayar sinadarin hydrocarbons a cikin tekun.

Sanarwar ta kara da cewa, kasashen duniya da dama sun bayyana aniyarsu na bada taimako domin magance tasirin barnar.

Jirgin ruwan yana dauke da albarkatun man fetur mai nauyin ton 750, ya nitse da yammacin ranar Juma’a a tekun Gabes dake kudu maso gabashin Tunisia, yayin da aka yi nasarar ceton dukkan matukan jirgin su bakwai.

Jirgin ruwan dakon man mai dauke da tutar kasar Equatorial Guinea, yana kan hanyarsa ne daga Masar zuwa Malta, wanda ya nemi izinin ratsa tekun na Tunisia sakamakon fuskantar rashin kyawun yanayi, yayin da matuka jirgin suka aike da sakon barazanar fuskantar hadarin daga nisan kilomita 11 daga yankin tekun Gabes, inda suka bayyana cewa, ruwa ya fara malale injin jirgin har ma ya fara nitsiwa da nisan mita biyu.(Ahmad)