logo

HAUSA

Amurka mai mulkin mulaka’u na kara hargitsa tsarin zaman lafiyar kasa da kasa!

2022-04-18 20:14:23 CMG Hausa

Tashin hankali na yaduwa a ko ina, Amurka na amfani da babakeren tattalin arziki, da hada hadar cinikayya, wajen kakabawa wasu takunkumi, tana kuma kafa kawance domin mayar da wasu saniyar ware a siyasance. Yadda Amurka take ma’amala da Rasha a wannan gaba, ya nuna irin dabarun ta na amfani da danniya, wajen rura wutar rikici, da tarwatsa tsarin zaman lafiyar kasa da kasa.

A shekarar 2003, Alfonso Cuaron, daraktan fim din “Harry Potter”, da “Prisoner of Azkaban”, ya kwatanta shugaban kasar Amurka na lokacin wato George W. Bush, da sarki “Voldemort” na cikin fim din Harry Potter.

A cewar marubuciyar fim din na "Harry Potter" J. K. Rowling, gwamnatin Amurka ta yi barna sama da wadda sarki Voldemort ya yi. Har ma cikin fushi ta taba furta cewa, “Kar a kuskura a fusata sarki Voldemort”!

A cikin fim din Harry Potter, sarki Voldemort mutum ne mai matukar ji da kan sa, da nuna rashin tunani wajen tabbatar da ya samu cikakken iko, wanda daga karshe hakan ne ya hallaka shi. Ta wannan mahanga, salon Amurka na nuna danniya, ba abun da zai haifar mata illa cutuwa.   (Saminu)