logo

HAUSA

Sin ta fara aikin gina wuri mai sanyi don adana riga-kafi a Masar

2022-04-17 15:58:33 CMG Hausa

Kamafin Sinovac na kasar Sin ya fara aikin gina wuri mai sanyi don adana alluran riga-kafi a wannan mako, ofishin jakadancin kasar Sin a Masar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Liao Liqiang, jakadan kasar Sin a kasar Masar, ya bayyana a wajen bikin kaddamar da fara aikin a ranar Alhamis cewa, ta hanyar tallafin kamfanin hada magungunan na kasar Sin, manyan dakuna masu sanyin zasu taimakawa kasar Masar wajen inganta aikin adana riga-kafin.

A cewar jakadan, wurin ajiyar mai fadin murabbi’in mita 2,800, yana da girman da zai iya daukar alluran riga-kafi miliyan 150 idan aikin ya kammala, kuma zai taimakawa kasar Masar wajen cimma burinta na yiwa kashi 70 bisa 100 na al’ummar kasar alluran riga-kafin COVID-19 nan da tsakiyar shekarar 2022.

Liao yace, wannan wata gagarumar nasara ce da aka cimma karkashin hadin gwiwar Sin da Masar a yaki da annobar COVID-19, kuma kasar Sin zata cigaba da karfafa hadin gwiwarta da Masar a fannin kiwon lafiya, sannan zata kara bada gudunmawa wajen kyautata zaman rayuywar al’ummar kasar Masar.

A lokacin bikin, Khaled Abdel Ghaffar, ministan ilmi mai zurfi da binciken kimiyya na kasar Masar, ya bayyana farin cikinsa tare da godewa gwamnatin kasar Sin, da al’ummar Sinawa, bisa goyon baya da taimakon da suke bayarwa a dogon lokaci don cigaban fannin kiwon lafiyar Masar.

Ghaffar ya ce, sabbin wuraren ajiyar masu sanyi, zasu karawa Masar kaimi wajen aikin samar da riga-kafin a cikin gida, da adanawa, da kuma rarraba riga-kafin, kana zai taimakawa kasar Masar don zama wata cibiyar samar da riga-kafi a Afrika da ma yankin gabas ta tsakiya.(Ahmad)