logo

HAUSA

Jadawalin aikin gina tashar binciken sararin samaniyar Sin a 2022: Karin ayyuka 6

2022-04-17 20:46:29 CMG Hausa

Wani jami’in hukumar ayyukan binciken sararin samaniyar kasar Sin ya bayyana a taron manema labarai a yau Lahadi cewa, ana fatan gudanar da jimillar ayyukan binciken sararin samaniya na kasar Sin kimanin shida a cikin wannan shekarar ta 2022, domin kammala aikin gina tashar sararin samaniyar ta kasar Sin.

Za a kaddamar da kashin farko na harba jirgin dakon kayayyakin binciken sararin samaniyar na Tianzhou-4 a watan Mayu, a cewar Hao Chun, daraktan ofishin kimiyya na hukumar binciken sararin samaniyar kasar, ya kara da cewa, za a harba jirgin binciken nau’in Shenzhou-14 a watan Yuni, tare da ‘yan sama jannati uku a babban rukuni wadanda kuma za a ajiye su a yankin sararin samaniyar na tsawon watanni shida.(Ahmad)