logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka harbu da COVID-19 da aka gano daga sassan birnin Shanghai da ba a kebe su ba ya ragu

2022-04-17 16:45:38 CMG Hausa

Yau da safe hukumar kula da kiwon lafiya ta birnin Shanghai na kasar Sin ta sanar cewa, ya zuwa ranar 16 ga wata, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 ya kai 3238, kana adadin mutanen da suka harbu da cutar, amma ba su nuna alamun cutar ba ya kai 21582.

Rahoton taron manema labarai game da aikin kandagarkin cutar na birnin Shanghai da aka shirya yau ya nuna cewa, daga cikin daukacin mutanen da suka harbu da cutar, amma ba su nuna alamar cutar ba, an gano mutane 21167 ne aka kebe su, yayin da mutane 415 ne kawai aka gano su daga sauran sassan birnin, yayin da ake tantance kwayar cutar, ana iya cewa, adadin mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 da aka gano daga sassan birnin da ba a kebe su ba ya ragu, duk da cewa, adadin mutanen da aka gano sun harbu da cutar bai ragu ba, amma shi ma bai karu zuwa adadi mai girma ba. (Jamila)