logo

HAUSA

Kasar Sin ta bayyana adawarta da ziyarar da wasu ‘yan majalisar Amurka suka kai Taiwan

2022-04-16 16:17:16 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya soki ziyarar da wasu ‘yan majalisar kasar Amurka suka kai yankin Taiwan na kasar Sin.

Wu Qian, ya bayyana a jiya Jumma’a 15 ga wata cewa, ziyarar wani salon takala ne da gangan, wadda ta yi tsananin take ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da kuma tanadin sanarwar hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka fitar.

Ya kara da cewa, munafurci ne da rashin gaskiya, Amurka ta ce ba ta goyon bayan ‘yancin kan Taiwan, a daya bangaren kuma, tana aike da wani mummunan sako ga masu rajin ballewa. Yana mai cewa, kasar Sin tana adawa da hakan, kuma ta gabatar da korafinta ga Amurkar.

Bugu da kari, ya ce rundunar sojin kasar Sin ta gudanar da wani sintiri shirin ko ta kwana da kuma horo a yankunan ruwa da sararin samaniyar tsibirin Taiwan.

Ya ce rundunar sojin kasar Sin, tana cikin shiri kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace na dakile duk wani kutse daga waje da kuma dakile yunkurin masu neman ‘yancin kan Taiwan. (Fa’iza Mustapha)