logo

HAUSA

Me Ya Sa MDD Ta Ayyana Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin Tamkar Babban Abin Koyi

2022-04-16 20:30:34 CMG Hausa

Yau Asabar da safe misalin da karfe 10, bangaren dawowa na kumbon Shenzhou-13 na kasar Sin ya sauka doron duniya lami lafiya. ‘Yan sama jannati 3 da ke cikin kumbon sun kammala aikinsu a sararin samaniya har na tsawon watanni 6, inda suka dawo gida.

Yayin da ake murnar samun nasarar dawowar ‘yan sama jannatin 3 na kasar Sin duniyarmu, abin da ya kamata a tuna da shi, shi ne da wuya  kasar Sin ta samu irin wannan nasara. Bayan da kasar Sin ta tsara manyan tsare-tsare na matakai 3 na ganin ‘yan sama jannati sun yi tafiya cikin kumbo a sararin samaniya a shekarar 1992, kasar Sin tana nacewa kan tsayawa da kafafunta a fannin yin kirkire-kirkire, ta kuma inganta hadin gwiwa da kasashen Rasha, Japan da Turai, a kokarin samun ci gaba a mataki-mataki.

Yau an samu cikakkiyar nasarar gudanar da aikin kumbon Shenzhou-13. Kasar Sin ta shiga matakin ginin babbar tashar sararin samaniya. Watakila nan da shekaru da dama masu zuwa, tashar za ta kasance tashar sararin samaniya daya tak a sararin samaniya, lamarin da zai zama babbar nasarar al’ummar kasar Sin ta fannonin kimiyya da fasaha, kana kuma zai zama mafarin sabon matakin nazarin sararin samaniya ga dukkan ‘yan Adam.

Har ila yau tashar sararin samaniyar kasar Sin za ta bude kofarta ga dukkan kasashe mambobin MDD a karo na farko a tarihi. Yanzu an tanadi ayyuka guda 9 daga kasashe 17 da rukunoni guda 23 cikin jerin ayyuka a rukuni na farko, wadanda za a gudanar da su cikin tashar sararin samaniyar kasar Sin. Dangane da lamarin, madam Simonetta Di Pippo, darektar ofishin kula da harkokin sararin samaniya na MDD ta bayyana cewa, tashar sararin samaniyar kasar Sin da za ta bude kofa ga kowa, wani muhimmin bangare ne na shawarar MDD ta yin amfani da sararin samaniya tsakanin kasa da kasa, ta kasance wani babban abin koyi. (Tasallah Yuan)