logo

HAUSA

Ministan wajen Ukraine da sakataren wajen Amurka sun tattauna ta wayar tarho

2022-04-15 13:50:29 CMG Hausa

A jiya Alhamis, ministan wajen Ukraine Dmytro Kuleba, da sakataren wajen Amurka Antony Blinken, sun tattauna ta wayar tarho, game da sabon tallafin kudaden gudanar da ayyukan soji ga Ukraine.

Cikin wani sakon Tiwita da ya wallafa, Mr. Kuleba ya ce yayin zantawar tasu, sun amince kan matsaya daya, don gane da kara kakabawa Rasha takunkumi, bisa zarginta da mamayar Ukraine. Ya kuma jinjinawa Amurka bisa jajircewarta wajen tallafawa Ukraine.

A ranar Larabar da ta gabata, shugaba Joe Biden na Amurka, ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta samarwa Ukraine karin kudin tallafin ayyukan soji da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 800, domin kasar ta samu damar dakile hare-haren da Rasha ke kaiwa yankuna masu yawa dake gabashin Ukraine.  (Saminu)