logo

HAUSA

Kasar Sin ta gargadi Amurka game da matakin da ta dauka kan batun Taiwan

2022-04-15 20:13:46 CMG Hausa

 

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana rashin amincewa da ziyarar da 'yan majalisar dokokin Amurka da dama suka kai yankin Taiwan na kasar Sin.

Rahotanni na cewa, 'yan majalisar dokokin Amurka guda shida, da suka hada da shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawan Amurka Bob Menendez na jam'iyyar Democrat, da Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican, sun sauka a Taiwan jiya Alhamis, kuma za su gana da jagorar yankin Tsai Ing-wen.

Zhao ya shaidawa taron manema labaran da aka shirya yau cewa, ya kamata 'yan majalisar dokokin Amurka, su martaba manufar “kasar Sin daya tak a duniya” da gwamnatin Amurka ta amince da ita, da kiyaye ka'idar “kasar Sin daya tak a duniya”, da kuma sanarwowin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, da dakatar da yin mu'amalar da ke tsakanin Amurka da yankin na Taiwan a hukumance. Haka kuma bai kamata su furta kalaman da ba su dace ba. Kasar Sin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai, da tabbatar da kare ikon mallakar kasa da cikakkan yankunanta.(Ibrahim)