logo

HAUSA

Rahoto ya nuna yadda ake samun karuwar nuna wariya ga ’yan Asiya a Amurka

2022-04-15 13:52:54 CMG Hausa

Kungiyar nazarin hakkil bil adama ta kasar Sin ta fidda rahoto a yau Juma’a, wanda ke nuna cewa, ana samun karuwar nuna wariya ga al’ummu ’yan asalin Asiya a kasar Amurka.

A cewar rahoton, har yanzu Amurka tana tinkaho da matsayinta na kasa mai hallayar nuna fifiko a tsakanin Amurkawa farar fata mafiya rinjaye, da sauran kananan kalibun kasar. Rahoton ya ce, Amurkawa ’yan asalin Asiya, da Amurkawa ’yan asalin Afrika, da ’yan Latino da kuma Amurkawa ’yan asalin Indiya, suna fuskantar nuna wariya da kyama a fannoni daban-daban, kuma ba sa iya samun cikakken hakkokinsu yadda ya kamata.

Rahoton ya kunshi bangarori kamar haka, Amurkawa ’yan asalin Asiya suna fuskantar hare-haren nuna wariya yayin da aka samu barkewar annobar COVID-19, kuma nuna wariya ga Amurkawa ’yan asalin Asiya ba wai ya takaita saboda annobar ba ne, akwai wasu dalilai da dama da suka kara ta’azzara nuna wariyar ga ’yan Asiya ta hanyar fakewa da annobar COVID-19.

A cewar rahoton, ana iya cewa, bayan kawo karshen annobar, ko da batun nuna wariya ga ’yan Asiya ya ragu, mai yiwuwa ne hare-haren da ake kaddamarwa kan Amurkawa ’yan asalin kasar Sin zai iya ci gaba da karuwa, sakamakon tasirin ’yan siyasar Amurka dake nuna kiyayya ga kasar Sin, inda aka bukaci daukar matakai mafi dacewa bisa tsarin kasa da kasa domin daidaita batun. (Ahmad)